Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Sarkin wanda ke da alhakin kula da Masallachin na Al Aqsa yayi gargadi ga Israila akan abinda ya kira takalar fada da jami’an ta keyi.
Ya kuma tattauna da bangarori da dama da batun ya shafa domin ganin an kawo karshen takurawar da jami’an tsaron Isra’ilar ke yi wa falasdinawa masu ibada a Al’Aqsa, daya daga cikin manyan wuraren ibadan Musulmi da kuma Yahudawa.
Masana dai na da fargaba akan irin matakan da Isra’ila ke dauka na takala a harabar masallacin na su ruguza kokarin samar da zaman lafiya na tsakanin Isra’ilar da Falasdinu.
Yau Talata an tsara kwamitin sulhu na MDD zai yi zama na musamman domin tattauna sabon tashin hankalin da aka samu a Birnin Kudus wanda ya kaiga raunana akalla mutane 170.
342/