Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wani sabon rikici ya barke ne bayan da wasu yahudawa suka shiga msallacin Kudus domin gudanar da bikin Passovar wanda yaci karo da lokacin Azumin watan Ramadan mai alfarmi da hakan ya kara ruruta wutar rikici tsakanin sojojin Isra’ila da falasdinwa agabar yammacin kogin Jodan wanda ya zuwa yanzu ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 36.
Kasashen larabwa da sauran yan siyasa ne suka yi tir da wannan matakin nuna fin karfi da israila take yi kan falasdinawa musamman a cikin watan Azumin ramadana mai alfarma,
Masallacin Kudus da farfajiyarsa sun shaidi rikici mai tsanani a shekarun bayan tsakanin sojojin Isra’ila da falsdinawa masu ibada,wanda yayi sanadiyar jikkata sama da falasdinawa 160.
A cikin zantawar tasu ta water tarho dukkan bangarorin biyu sun nuna fatansu na ganin yanayin da ake ciki bai yi muni ba da zai kara tsananta rikici tsakanin falasdinawa da sojojin Isra’ila, kana kuma sun tattauna kan dangantakar dake tsakaninsu da kuma yadda zasu yi aiki tare a bangarorin ciniki da tattalin arziki .
342/