Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - An kaddamar da gagarumin gangamin na miliyoyin mutane ne domin tunawa da ranar 11 ga watan Afirilu wato lokacin hambarar da gwamnatin Albashir, kamar yadda kuma suka nuna rashin amincewarsu da ci gaba da yin babakere da sojoji ke yi a kan mulkin kasar.
Ganin yadda jama’a ke ta matsin lamba a kan hukumar soji, kwamitocin adawa sun fara tsara sahunsu, tare da yin watsi da duk wasu bambance-bambancen da ke tsakaninsu, tare da hada kansu domin tunkarar mataki na gaba.
Sojojin kasar Sudan dai sun kwace mulki ne bayan da al'ummar kasar suka nuna rashin gamsuwa da mulkin Alabshir, tun daga lokacin kuma suke ci gaba da mamaye madafun iko na kasar.
342/