Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ‘Yan majalisa 174 daga cikin 342 ne suka kada kuri’ar yanke kauna ga Imran Khan, kamar yadda shugaban majalisar na riko Sardar Ayaz Sadiq, ya sanar.
Wannan wata nasara ce da bata zo da mamaki ba ga kawancen ‘yan adawa na kasar dake da suka samu rinjaye a majalisar a kwanakin baya baya nan.
A Pakistan dai babu wani firaminista da ya taba kammala wa’adinsa tun bayan samun ‘yancin kai na kasar a 1947, amma Imran Khan dake shugabacin gwamnatin kasar tun 2018, shi ne wani firaminista da aka tsige ta hanyar kuri’ar yanke kauna.
A makon da ya gabata dai bangaren dake goyan bayan Imran Khan, sunki amince mika bukatar tsige shi, tare da rusa majlaisar dokokin kasar, saidai daga bisani kotun tsarin mulki ta kasar ta yi watsi da matakin tare da dawo da majalsiar da kuma amince kada kuri’ar da ta kai ga tsige Imran Khan din.
Masana dai na ganin akwai barazanar kasar ta fada wani rikicin siyasa da ba’a san lokacin karewarsa ba.
342/