Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kungiyar ta Ecowas ta fadi cewa wannan wani bangare ne na jin kai ga gwamnatin Najeriya domin tallafawa iyalan wadanda rike-rikice suka shafa a Arewa mai kudu da arewa masu gabashin Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa za ta yi aiki tare da hukumar samar da abinci ta duniya wajen amfani da tallafin domin shawo kan matsalar karancin Abinci mai gina jiki da ake fuskanta a jihohin Katsina Zamfara da kuma Borno
Shirin zai bada tallafin injunan nika tare da horas da yan gudun hijira 603 da suka dawo daga kasar kamaru da kuma matan karkara da suka rasa gidajensu da kuma tallafa musu da hanyoyin samun kudaden shiga domin ci gaba da rayuwarsu
342/