Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shirin MDD dake tallafawa Sudan wato (UNITAMS), ya bayyana damuwa game da karuwar tashe-tashen hankula na baya bayan nan a yankin Darfur, wanda ya yi sanadiyyar hasarar gomman rayukan fararen hula, da mutuwar masu zanga-zanga biyu a babban birnin kasar Khartoum.
Tun da farko, kafafen yada labaran cikin gidan kasar, sun bayyana cewa, fadan kabilanci da ya barke a ranar Alhamis a yankin Jebel Moon a jahar Darfur ta yammacin kasar Sudan, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 17.
342/