12 Maris 2022 - 13:41
AU Da MDD, Na Hadin Guiwa Domin Samar Da Mafita Ga Rikicin Sudan

Kungiyar tarayyar Afrika da Majalisar Dinkin Duniya, sun ce suna hadin guiwa a tsakaninsu domin samar da wata mafita ta siyasa ga rikicin da ya ki ci yaki cinyewa a Sudan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - An dai kasa samun sukuni a Sudan tun bayan rikicin da ya barke sakamakon juyin mulkin ranar 25 ga watan Oktoban da ya gabata.

Har yanzu ana ci gaba da zanga zangar kin jinin mulkin sojojin a kasar ta Sudan, yayin da jami’an tsaron ke ci gaba da amfani da karfi wajen murkushe masu zanga zangar.

Babban abunda suka sanya a gaba shi ne, dawo da aiki da kundin tsarin mulkin kasar da kuma kawo karshen juyin mulkin soji.

Tuni dai Kawancen dake fatan samar da sauyi a kasar ta Sudan ya yi maraba da matakin hadin guiwar na MDD da kuma AU, wadanda a cen baya suke ayyukansu daban daban.

342/