Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wanann ita ce ziyara ta uku ta Rapael Grossi, karkashin sabuwar gwamnatin Iran.
Yayin ziyarar tasa M. Grossi, ya gana da takwaransa na Iran, Mohammad Eslami, inda suka jagoranci wani taron manema labarai.
Eslami ya bukaci hukumar ta IAEA da ta ba da hadin kai ta fuskar siyasa.
A nasa bangare Grossi ya ce ya kasance yana tattaunawa da takwaransa na Iran akai-akai, amma bangarorin biyu suna dan sabani kan wasu batutuwa amma zasu ci gaba da aiki domin ganin sun waraware sabanin.
Ziyarar ta M. Gross, ta zo ne a daidai lokacin da ake tattaunawar Vienna da nufin ceto yarjejeniyar nukiliayar 2015, kuma a cewarsa idan Iran da IAEA ba su cimma matsaya ba, zai yi wuya a cimma wani abu a babban birnin kasar Ostiriya.
342/