Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaban jami’ar “ Bakiyyatullah” ta aikin likitanci wacce ta samar da maganin Hasan Abul-kasim ya fadawa kamfanin dillancin labarun Irna cewa; Samar da sabuwar allurer wani Karin daraja ne ga masu bincike da nazari na aikin likitanci na Iran, wanda yake nufin dogaro da kai.
Abul-kasim ya cigaba da cewa; Ina bai wa ‘yan kasa tabbacin cewa za su iya yin amfani da allurar rigakafin ta Nura ba tare da wata damuwa, domin gwaje-gwajen da aka yi sun tabbatar da ingancinta, kuma da karfi wajen maganin Corona.
Wani jami’in ma’aikatar kiwon lafiya ta Iran ya tabbatar da cewa; Allurar rigakafin ta Nura,ta bayar da sakamako mai karfi wajen fada da cutar ta korona a yayin gwaje-gwajen da aka yi.
Wannan dai ita ce allurer rigakafin cutar korona ta shida dam asana a Iran su ka samar da ita. Sauran sun hada Fakhra, Barkat, Pastor, Razy, Spaicojin.
342/