25 Faburairu 2022 - 20:10
Sabon Pira mininstan kasar Libya ya sanar da sunayen wadanda ya zaba domin kafa gwamnati

Fathi Bachagha ya sanar a jiya Alhamis cewa; Ya kammala zabar wadanda zai yi aiki da su a cikin gwmanatinsa, kuma zai aike da sunayen nasu zuwa ga ‘yan majalisa domin bayar da goyon baya da amincewa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Fathi ya ce; Sunayen sabbin jami’an gwamnati ya gama kammaluwa, kuma za a tura shi zuwa ga ‘yan majalisar dokoki domin amincewa da shi.

Wata majiya ta ambaci cewa gabanin zabar sunayen wadanda za su kasance a cikin gwamnatin tashi, ya tuntubi bangarori daban-daban na ‘yan siyasar kasar.

Tun bayan da aka dage lokacin zaben da aka tsayar za a yi a baya, kasar Libya ta sake fuskantar sabani a tsakanin ‘yan siyasarta inda aka nada pira ministoci biyu.

Sai dai a halin yanzu ana tsammanin samun mafita daga dambaruwar siyasar da kasar ta kasance a ciki tun bayan kashe Mu’ammar Kaddafi a 2011.

Kawo ya zuwa yanzu dai babu lokacin da aka tsayar domin majalisar kasar ta yi zaman tantance sabbin mambobin gwmanatin.

342/