Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - M. Bennett zai gana da yarima mai jiran gado na Bahrain kuma firaminista Salman bin Hamad al-Khalifa, in ji ofishinsa.
A cikin wata sanarwa da shugaban ya fitar, ya ce, "shugabannin za su tattauna kan karin hanyoyin karfafa huldar dake tsakanin kasashen biyu...musamman ciyar da harkokin diflomasiyya da tattalin arziki gaba, tare da mai da hankali kan fasaha da kirkire-kirkire.
" Ana kuma sa ran Naftali Bennett zai gana da wakilan al'ummar Yahudawan Bahrain a cewar ofishinsa. Ziyarar ta biyo bayan wata ziyarar da ministan tsaron Isra'ila Benny Gantz ya kai Manama a farkon watan nan, inda kasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro.
342/