Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ya ce: “Muna kallon abin da ke faruwa a kasa, dole ne mu ga dabi'un Amurkawa game da cire takunkumi a aikace ba magana ta fatar baki ba."
Kalaman na zuwa ne kwanaki biyu bayan da gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden ta yi ikirarin cewa za ta cire takunkumin da aka sanya ma Iran, wanda Donald Trump ya sake maido da su a watan Mayun 2020.
Amir-Abdollahian ya ce Iran ba ta samu wani abu rubuce daga bangaren Amurka ba, duk da ikirarin da wasu kafafen yada labarai suka yi a baya-bayan nan kan batun cirewa Iran takunkumai.
342/