26 Janairu 2022 - 17:13
Yemen Ta Gargadi UAE Kan Cewa Zata Rugurguza Dubai Expo 2020 A harinta Na Gaba

Kakakin sojojin kasar Yemen ya gargadi gwamnatin kasar UAE kan cewa idan bata dakatar da hare-haren da take kaiwa mutanen kasarsa a cikin kawancen Saudiya ba, to hare-harenta na gaba zata wargaza shahrerren ginin nan mai suna ‘Dubai Expo 2020’ a hare-haren maida martani da take yi kan kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Burgediya Janar Yahya Saree yana fadar haka a shafinsa na twitter a jiya Talata. Ya kuma kara da cewa UAE ta yi hattara da sojojin kasar Yemen don zasu jawo mata asarorin da ba zata yi tsammani ba.

Masana dai suna ganin wannan gargadine ga ita UAE da kuma kamfanonin da suke kawance da ita a harkokin kasuwanci a wadannan manya-manyan cibiyoyi a birnin Dubai ne. Kafin haka dai Yahyah Saree ya gargadi kamfanonin kasashen waje a kasar UAE da su su san cewa suna cikin hatsari.

342/