Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Dangote ya sanar da cewa kafanin mai din zai fara Aiki a kashi Ukku na wannan shekarar, ana sa ran kamfanin zai kawo gagarumin sauyi kuma zai kara karfafawa wajen bunkasa tattalin arzikin da hadinkai tsakanin kasashen yankin, da farko dai zai farad a Sarrafa ganga 540,000 na danyen man fetur a kowacce rana, kuma nan da shekara ta 2023 zai kai ga yawan adadin da yake sun tacewa a duk rana
Ya ce zuwa shekara ta 2023 matatar mai din za ta taimakawa Najeriya ta dakatar da shigo da tataccen man fetur daga kasashen ketare , masana na ganin wannan babban albishir ne ga kasa mai dinbin arzikin mai amma tana fama da matsalar karanci mai a cikin gida.
Ana sa bangaren shugaban bankin raya tattalin arzikin Afrika Adesina ya bayyana wannan mataki amatsayin wani sabon shiri na kawo gagarumin sauyi, kana yayi kira ga kasashen yankin da su taimaka wajen ci gaban masana’antu a nahiyar baki daya.
342/