Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Na’urorin da suka kunshi kyamarori na zamani masu hango duk wani motsin dan adam a cikin dare kirar kasar Rasha, su ne irinsu na farko da aka girke a Afrika.
Wannan ya kara nuna yadda dangantaka tsakanin kasashen biyu ke dada Kamari.
Iyakar Aljeriya da Morocco ta kasance a rufe na tsawon kusan shekaru 25, kuma ita ce wata iyaka ta tsakanin kasashen labarawa biyu da aka fi sanya ido sosai.
Aljeriya dai na daukar batun tsaron iyakarta da Morocco da matukar mahimmanci wanda take dangantawa da yankin sojoji, wanda ta ce ana amfani da shi wajen fasa kwabrin makamai dake fadawa hannun gungun kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Bayanai sun ce ko a baya bayan nan ma Morocco ta girke makamai akan iyakarta da Aljeriya.
Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta dada Kamari ne tun bayan ziyarar da ministan tsaron Isra’ila ya kai Morocco.
Morocco dai ta dawo da alakarta da Tel Aviv, yayin da Alejriya ke ci gaba da nuna goyan bayanta ga Falasdinu.
342/