Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, shugaban ya gana da tokwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, inda suka tattauna batutuwa da dama, daga ciki har da karfafa dankon zumunci tsakanin kasashen biyu, tattalin arziki, tsaro da kuma siyasar kasa da kasa.
Har’ila yau ana saran shugaba Ra’isi zai yi jawabi a majalisar dokokin kasar Rasha 'Duma', sannan zai gabatar da jawabi a Jami’ar Mosco.
Banda haka an tsara cewa shugaban zai gana da Iraniyawa ma zauna kasar Rasha da kuma malaman addini -shia da Sunna- kafin ya kammala ziyararsa a ranar Jumma’a.
342/