Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shiga tsakani da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na ƴan makonni ya sa an mayar da Firaiminista Abdalla Hamdok kan muƙaminsa, sai dai ajiye aiki da ya yi a makon da ya gabata ya ƙara jawo damuwa da shiga halib rashin tabbas kan makomar siyasar Sudan da kuma batun miƙa mulki bayan zaben da ake sa ran za a yi a 2023.
Wakili na musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya a Sudan Volker Perthes ya bayyana cewa duk matakan da aka ɗauka a baya har zuwa yanzu ba su yi aiki ba.
Ƙungiyoyi daban-daban dai da jam'iyyu sun gudanar da zanga-zanga inda suke cewa babu batun sulhu, zanga-zangar da ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 60.
342/