Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaban ya kara da cewa, Shahid Sulaimani bakon firai ministan kasar Iraki ne a lokacinda yay a shahada, don haka gwamnatin Amurka ta keta hurumin gwamnatin kasar Iraki a lokacinda ta kashe bakonta a cikin kasar ba tare da tuntubar ta ba.
Daga karshe shugaban ya kara da cewa idan da za’a sami wata kotu a duniya wacce zata gurfanar da tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump da Mike Pompeo da kuma wasu wadanda suke da hannu a cikin wannan kissan, da yana da kyau, amma ko da hakan bai samu ba muna fatan lokaci zai da za’a daukin fansar kissan wadannan shahidai.
Shahadar ta su ta shiga cikin kundin tarihin duniya kan cewa su ne suka wargaza makirce-makircen Amiurka a yankin gabas ta tsakiya.
342/