Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Mai magana da yawon ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran Saeed Khatibzadeh ya bayyana hakan ne a yau a lokacin ganawa da manema labarai a birnin Tehran, inda ya bayyana cewa, tattaunawar tana gudana bisa yin la’akari da shawarwarin da Iran ta gabatar.
Ya ce akwai babtutuwa wadanda suka shafi batun Amurka wadda ta fice daga yarjejeniyar, wanda kuma ana bin komai daki-daki domin kada a sake samun wani bangare ya yi gaban kansa kamar yadda Amurka ta yi a baya, domin tabbatar da hakan a mtsayin daya daga cikin ka’idoji na yarejeniyar.
Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, akwai wasu lamurra da suka shafi Iran da China da kuma Rasha, wadanda ko da an cimma wata matsaya, a Vienna, abubuwan da suke tsakanin Rasha da China ba za su canja ba, ta fuskar cinikayya da sauran harkokin tattalin arziki.
Khatibzadeh ya kamma da cewa, ga dukaknin alamu dai kasashen turai sun fahimci kuren da suka tafka, na tunanin cewa yin matsin lamba kan Iran zai iya tailasta ta janye daga matsayinta, inda yanzu sun fara dawowa daga rakiyar irin wannan tunani, domin kuwa sun gane cewa ba abu ne da zai taba yiwu ba.
342/