Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Rahotanni daga hedikwatar tsaron kasar na nuni cewa a wannan barin wuta na ranar Asabar dakarun kasar 11 ne suka kwanta dama.
Babban hafsan sojan kasar Janar Gilbert Ouedrago ya jajantawa iyalan sojojin tare da ziyartar wadanda suka samu raunuka wadada suke kwance a asibitia halin yanzu.
Tun a shekara ta 2015 ne kasar ta Burkina Faso ta fuskanci hare-haren yan ta’adda da suka hadasa asarar rayukan jama’a tare da tilastawa da dama tserewa daga yankunan su.
Mayakan ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi da ke cikin kasar Mali ne suke yin barazana ga zaman lafiyan kasar ta Burkina Faso.
342/