Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ne ya sanar da rasuwar tasa cikin wata sanarwa a wannan Lahadin.
Ba’a dai bayyana dalilin mutuwar tasa ba, saidai an ce ya rasu a wani asibiti dake birnin Captown.
Tuni dai kasashen duniya suka fara aikewa da sakon ta’aziyya game da mutuwar malamin.
Firaminitan Biritaniya, Boris Jonson, ya wallafa a shafinsa na twitter cewa za’a rika tunawa da dattakon da Archbishop Desmond Tutu ya rayu da shi a tsawon shekaru.
Shi kuwa shugaba Emanuel Macron na faransa cewa gwagwarmayar Desmon Tutu, za ta tsaya a tunaninmu.
342/