23 Disamba 2021 - 13:14
​Iran: An Shiga Kwana Na Uku A Atisayen Rasulul Akram Na 17 A Kudancin Kasar

Yau kwanaki uku a kenan hadin giwan sojojin IRGC na kasar Iran suke gudanar da atisayen sojoji mai suna “Rasulul Azam 17” a gabar tekun Farisa da kuma wasu wurare a kudancin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya bayyana cewa a wannan karon sojojin sun yi wasan wuta don samar da kariya ga tsibiran kasar Iran da yankuna bakin ruwan tekun faraisa. Kuma sun gwada sabbin makamai a wannan atisayen.

Sojojin sun yi amfani da tsibirin Larak da ke cikin tekun farisa don aiwatar da atisai na yau Laraba. Sun kuma tabbatar da ingancin makamai da kayakin yakin da suke amfani da su.

342/