22 Disamba 2021 - 13:30
​Har Yanzu Babu Tabbas Game Da Zaben Libiya

A kasar Libiya, yayin da ranar babban zaben kasar ke kara karatowa har yanzu babu tabbas akan cewa ko za’a gudanar da zaben a ranar 24 ga watan Disamba kamar yadda aka tsara.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Ko da yake babu wata sanarwa a hukumance da ta ce an dage zaben, amma alamu na nuna cewa da yuwa zaben ya gudana kamar yadda aka tsara.

A cikin kwana biyu da suka rage har yanzu ba’a sanar da sunayen ‘yan takara na dindindin da zasu fafata a zaben, kana har yanzu akwai rarrabuwar kai tsakanin bangarorin dake rikici a kasar.

Lamarin da tuni masana ke ganin cewa zai iya kara jefa kasar cikin wani sabin rikici.

Ko a ranar Litini, rahotanni sun ce an ga wasu gungun masu dauke da makamai dake biyaya ga ministan tsaron kasar sun toshe hanyoyin shiga Tripoli babban kasar da motoci masu sulke.

342/