Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto ministan yana wannan maganar ne, a lokacin zantawarsa da babban sakataren MDD Antonio Guterres a jiya Laraba. Abdullahin ya kara da cewa Iran ta gabatar da bukatunta ga kasashen da suka rage a yarjejeniyar JCPOA da kekyawar nufi, don a cimma matsaya kan bukatar Amurka na komawa cikin yarjejeniya da ta bari a shekara ta 2018. Amma wasu kasashe turai suna maganganu wadanda suke yin barazana ga kasar Iran. Kuma sun san cewa barazana bata taba aiki a kan Iran ba.
342/