Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Jaridar The Nation ta kasar Kenya ta bayyana cewa shuwagabannin sun dauki wannan matsayan ne a taronsu na jiya Lahadi a cibiyar kungiyar dake birnin Abuja na tarayyar Najeriya.
Labarin ya kara da cewa idan har kungiyar bata ga alamar cewa gwamnatin sojoji ta kasar Mali tana shirin gudanar da zabubbuka ba, to zata kara dora mata takunkuman tattalin arziki.
Shuwagabannin sun sanya ranar 27 ga watan Fabreru na shekara ta 2022 a matsayin ranar ta karshe na gudanar da zabubbuka a kasar ta Mali.
Kafin haka dai shugaban kasar ta Mali yay i alkawarin zai mikawa kungiyar jadawalin zaben a cikin watan Jeneru mai zuwa.
Banda haka shugaban kasar ta Mali Kanar Assimi Goita ya dage lokacin zaben zuwa wani lokacin da bai ambata ba, sannan mai makon haka zai kafa wata majalisa ta shawarwari.
A cikin watan Augustan shekara ta 2020 ne Goita ya jagoranci juyin mulki wa zabebben shugaban kasa Ibrahim Bubakar Kaita, sannan a cikin watan mayun shekara ta 2021 ya saje yiwa shuwagabannin gwamnatin rikon kwarya juyin mulki.
342/