Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- na kasar Iran ya nakalyo shugaban hukumar gidajen radiyo da talabijin na kasar Iran Peman Jebelli yana fada haka a jiya Alhamis ya kuma kara da cewa ta’asan da kasar Burtaniya ta aikata a yakin duniya na biyu ya shiga cikin tarihin kasar Iran har’abada.
Daga cikin farin da mamayar da sojojin burtaniya suka yiwa kasar Iran a lokacin ya jawo ya na cikin tunanin maza da mata har da yaran kasar Iran, kuma zai ci gaba da zama cikin tabo a kan kasar Burtaniya har abada.
Kafin haka dai gwamnatin kasar Burtaniya ta kauracewa shahrerren dan jaridan nan san kasar Iran mai suna Ali Rezvani don abinda ta taimakawa wajen tace bayanai daga iraniyawa wadanda ake tuhuma da laifuffukan cin amanar kasa, wanda daga baya ake amfani da su wajen tabbatar da laifi a kansu a gaban alkali.
Gwamnatin Burtania ta haramtawa Ali Rezvani zuwa kasar Burtania’ sannan idan yana da waswu kadarori a kasar an kwace su.
342/