Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Abiy Ahmed wanda aka bawa kyautar Nebel kan zaman lafiya ya bayyana cewa sojojin gwamnatinsa da masu gaya masu baya sun sami nasarori da dama kan mayakan yan tawayen na Tigray a fafatawarsu a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.
Ahmed ya ce dole ne mayakan na Tigray su mika kai ga sojojin kasar ta Habasha da mayakan sa kai wadanda suke taimaka masu a wannan yakin.
A ranar Lahadin da ta gabata dai kafafen yada labarai na gwamnatin kasar sun bada sanarwan nasarorin da sojojin Abiy Ahmed suka samu a yankin Chifra a kuma garin Afar, sannan wannan nasarar zata ci gaba har zuwa lardin Amhara.
A makon da ya gabata dai kasashen yamma daga ci har da Amurka sun bukaci mutanen kasashensu da suke birnin Adis Ababa su bar kasar saboda karatowar mayakan yan tawaye na Tigray zuwa babban birnin Kasar, amma gwamnatin Abiy Ahmed ta ce babu wata barazana ga babban birnin kasar.
342/