28 Nuwamba 2021 - 14:36
Shugaban Iran Ya Gana Da Takwaransa Na Turkmenistan

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya gana da tokwaransa na kasar Turkmenistan Gurbanguly Berdymukhameduv a jiya Asabar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : kasar Iran ya bayyana cewa shugaban ya isa birnin Ashgabad babban birnin Turkmenistan ne a jiya da yamma kuma shgaban kasar ne ya yi masa maraba jim kadan bayan isarsa. A yau Lahadi ne za’a bude taron kungiyar kasashen ECO na tattalin arzikin a kasar ta Turkmenistan, wanda zai hada shuwagabannin kasashe 10 mambobi a cikin kungiyar. Banda jawabin da zai gabatar a taron shugaba Ra’isi zai gana da sauran shuwagabnnin kasashen da suka halarci taron, da iraniyawa mazauna kasar Turkmenistan har'ila yau da kuma ‘yan kasuwa. Kasashen 10 wadanda suka kafa kungiyar ECO ta raya tattalin arzikin kasashen dai, su ne Iran, Turkey, Pakistan, Afghanistan, Turkmenistan, Kyrgyzstan, Uzbekistan, Kazakhstan, Tajikistan, da kuma Azerbaijan.

342/