21 Nuwamba 2021 - 15:32
Iran: ​IRGC Sun Kama Wani Jirgin Ruwa Da Ke Fasakwabrin Man Diesel A Tekun Fasha

A yau ne dakarun kare juyin musulunci na Iran IRGC suka kama wani jirgin ruwa mallakin wata kasar waje dake dauke da man dizel da kuma mutane 11 da suka shiga yankin ruwan Iran a gabar kudancin tekun farisa da ke lardin Hurmusgan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A nasa bangaren Kanar Ahmad Hajian babban kwamandan sojan ruwa na zulfiqar 412 ya fadi cewa bayan gudanar da bincike a cikin jirgin ruwan sun samu man dizel da ya kai lita 150,000 kuma an mika mutanen 11 daga ciki har da matukan jirgin ga ofishin wani alkali dake wani gari a gabar tekun na farisa.

Hajian ya kara da cewa dakarun da yake jagoranta su na cikin shiri na dakile duk wani yunkurin yin fasakwabrin man dizal a cikin teku, don kara karfafa tattalin arzikin kasar.

A wata ziyara da major janar Salami kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran ya kai barikin sojojin ruwa dake arewacin kasar, ya fadi cewa Iran ta samu fasahar zamani na yaki a teku, kuma ba za ta yi kasa a guiwa wajen mayar da martani kan duk wani wuce gona da iri a cikinsa ba.

342/