19 Nuwamba 2021 - 11:02
ECOWAS Ta Sanya Wa Manyan Jami’an Mali 150 Takunkumi

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ECOWAS, ta sanya wa wasu manyan jami’an kasar Mali 150 da iyalansu takunkumi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jami’an sun hada da firaministan Mali, Choguel Maïga, da gabadayen mambobin gwamnatinsa.

Matakin ya tanadi haramta wa mutanen taba kudadensu da kuma hana su tafiye tafiye a kasashe mambobin kungiyar.

Saidai matakin bai shafi shugaban mulkin rikon kwaryar sojin Malin ba, Kanal Assimi Goita da ministan harkokin wajen kasar Abdoulaye Diop ba.

Kungiyar ta ECOWAS, dai ba ta yi bayyani ba kan dalilin tsame jami’an biyu ba daga jerin wadanda aka kakaba wa takunkumin.

Saidai wasu majiyoyin sun ce tsame su daga wadanda aka sanya wa takunkumi zai basu damar halartar tarukan kungiyar ta ECOWAS, da kuma bada damar ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin.

A farkon watan nan ne ECOWAS, ta dauki matakin na sanya wa jami’an Mali takunkumu saboda rawar da ta ce suke takawa wajen rura rikicin kasar bayan juyin mulki da sojoji sukayi wanda kuma yake kawo tarnaki wajen gudanar da zaben zabubukan kasar kamar yadda aka tsara a watan Fabarairun badi.

342/