Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Rahotanni daga Iraki sun sun tabbatar da cewa, ‘yan sa’oi bayan kai da aka yi a kan gidan Firayi ministan kasar Iraki Mustafa a Alkazimi a cikin daren Asabar da ta gabata, da jijjifin safiyar lahadi babban kwamandan dakarun Quds reshen dakarun kare juyin juya halin muslunci na Iran janar Qaani ya isa birnin Bagadaza, inda ya shiga tattaunawa kai tsaye tare da manyan jami’an gwamnatin Iraki, da suka hada da shugaban kasar Barham Saleh, da kuma Firayi ministan kasar Mustafa Alkazimi.
Bayan nan kuma Janar Qaani ya gana da wasu daga cikin kwamnadoji dakarun sa kai na al’ummar kasar Iraki, inda ya jadadda wajabcin hada karfi da karfe tsakanin dukkanin bangarori, da kuma dafa ma gwamnatin ta Iraki wajen fuskantar mawuyacin halin da ake kokarin jefa kasar.
Babbar manufar ziyarar Qaani a kasar Iraki dai ita ce, daukar matakan gaggawa daga bangaren kasar Iran wajen taimaka wa Iraki, biyo bayan wannan yunkuri.
342/