2 Nuwamba 2021 - 14:42
​Gharib Abadi: Rashin Magana Na Karfafa Gwiwar Isra'ila Wajen Aikata Laifukan Yaki

Sakataren majalisar koli ta kare hakkin dan Adam na kasar Iran Kazim Gharib Abadi a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na twiter a daren jiya, ya fadi cewa Gum da baki da kungiyoyin da ake kira na kare Hakkin bil dama ke yi kan muggan laifukan da Isra’ila ke tafkawa ne ke kara mata tsaurin ido da ya sa ta yaga rahoton da shugaban babban zauren majalisar dinkin duniya ya fitar akan Isra’ila,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Har ila yau Kazem ya fadi cewa rahoton ya kunshi binciken da kwamitin da majalisar ta kafa ya gabatar wanda aciki yayi tir da Isra’ila game da take hakkokin dan Adama da take yi, wannan shi ne karo na biyu da jakadan Isra’ila ya aikata haka tun na shekara ta 1975 bayan da majalisar dinkin duniya ta sanar da gwamntin sahayuniya a matsayin gwamnatin nuna wariya .

Daga karshe ya nuna cewa wannan mataki da jakadan Isra’ila ya dauka na yaga rahoton da kwamitin ya fitar bayan binciken da ya gudanar ya nuna cewa lallai akwai bukatar a ci gaba da binciken har sai gaskiya ta yi halinta,

342/