Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Sakin da mahukuntan Sudan suka yi masa a ranar Lahadin da ta gabata da wasu tsoffin jami’an gwamnatin kasar, ya sanya ayar tambaya game da muhimmancin wannan mataki, a daidai lokacin da kasar ke cikin rudanin siyasa da ba a taba yin irinsa ba, bayan da sojoji suka kwace mulki a makon da ya gabata.
Ghandour ya karbi mukamin ma'aikatar harkokin wajen kasar ne a zamanin Al-Bashir, baya ga shugabancinsa na rusasshiyar jam'iyyar "National Congress", wadda ita ce jam'iyya mai mulki a Sudan a lokacin.
A ranar Lahadin da ta gabata ma hukumomin kasar Sudan sun saki Muhammad al-Tabidi, tsohon daraktan yada labarai a hukumar tsaro da leken asiri a zamanin tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir.
342/