Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jaridar Egypt Today ta kasar Masar ta bayyana cewa a ranar 8 ga watan Satumban da ya gabata ne ministocin harkokin waje na kasashen Lebanon, Masar Jordan da Siriya suka gudanar da taro a birnin Amman na kasar Jordan inda suka amince da kaiwa kasar Lebanon iskar gas wanda bututunsa zai ratsa kasashen Jordan da Siriya.
Kafin haka dai jakadiyar kasar Amurka a Lebanon ya fadawa shugaban kasar Michel Awun kan cewa Amurka zata taimaka a kawowa kasar Lebanon gas daga kasar Masar bayan da kungiyar Hizbullah ta kasar ta sami nasarar shigo da makashi kasar daga kasar Iran.
342/