1 Nuwamba 2021 - 14:22
ECOWAS Za Ta Shirya Taro Kan Batun Mali Da Guinea

Shugabannin kasashe mambobin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, zasu gudanar da wani taron gaggawa a ranar 7 ga watan Nuwamba, a birnin Accra, domin waiwaye kan halin da ake ciki a kasar Guinea game da mulkin rikon kwarya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A ranar Juma’a data gabata dai wata tawagar kungiyar ta ziyarci kasar ta Guinea.

Taron zai kuma maida hankali kan mulkin rikon kwarya a Mali, inda ake ci gaba da fuskantar tada jijiyoyin wuya tsakanin kungiyar ta ECOWAS da kuma sojojin dake rike da mulki, wanda har ya kai ga Mali ta kori wakilin ECOWAS din daga kasar.

Kasar Ghana wacce ke rike da shugabancin karba karba na kungiyar ta ECOWAS, ita ce ta kira taron na gaggawa domin duba halin da ake ciki a kasashen biyu inda sojoji ke rikon kwarya.

Yayin ziyararar da ya kai a ranar 17 ga wata a Bamako, shugaba Nana Afuko Addo, ya bukaci lalle lalle hukumomin Mali dasu mutunta lokacin da aka tsayar na gudanar da zabe.

A ranar 27 ga watan Fabarairun badi ne aka shirya gudanar da manyan zabukan na Mali, da suka hada da na shugaban kasa, da na ‘yan majalisar dokoki, saidai sojojin dake rike da mulkin na Mali, sun ce suna son gudanar da taron kasa, kafin su tsayar da ranar gudanar da zabe.

342/