Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Manufar taron shi ne hada kai don taimakawa wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin kudancin Asiya.
Mahalarta taron na Tehran sun hada da ministocin harkokin wajen Iran, Pakistan, Turkmenistan, Tajikistan da Uzbekistan, da jakadun Rasha da China.
Sai kuma ministocin harkokin wajen China da na Rasha da ake sa ran zasu halarci taron ta kafar bidiyo.
Taron shi ne irinsa na biyu na kasashen shida makobtan kasar ta Afghanistan.
Yayin taron ministan harkokin wajen kasar Iran, Hossein Amir-Abdollahian ya bukaci taron da ya mayar da hankali kan halin da ake ciki a Afghanistan.
Ya ce yawancin matsalolin da Afganistan ke fuskanta a halin yanzu sun samo asali ne saboda shishigi na kasashen waje, musamman Amurka wacce dole ne a cewarsa ta amince da alhakin ta'addancin da ta yi a Afganistan cikin shekaru ashirin da suka gabata.
Amir-Abdollahian ya kara da cewa Iran na goyon bayan kafa gwamnati wacce za ta kunshi kowa da kowa a kasar ta Afghanistan.
342/