25 Oktoba 2021 - 14:29
Ana Zaman Dar-dar Bayan Juyin Mulki A Sudan

Kungiyar tarayyar Afrika ta bukaci da a saki dukkan jami’an siyasa da ake tsare da Sudan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A wata sanarwa da shugaban kwamitin kungiyar ta AU, Musa Faki Mahamat, ya fitar a wannan Litini, ya nuna matukar damuwarsa akan mummunan halin da aka shiga a Sudan, bayan cafke firaministan kasar Abdollah Hamdok da kuma wasu manyan ‘yan siyasa.

Ya kuma bukaci a gaggauta tattaunawa tsakanin sojoji da fararen, wacce ita kadai hanyar da zata ceto kasar a cikin halin data tsunduma.

Yanzu haka dai an shiga zaman dar-dar a kasarta Sudan, bayan da rahotanni suka ce an yi yunkurin juyin mulki aka kuma kame mambobin gwamnatin rikon kwarya.

Fira ministan kasar Abdallah Hamdok, da wasu ministoci hudu na daga cikin wadanda aka yi amanna cewa wasu sojoji da ba a tantance ko su waye ba sun kama tare da tsare su a safiyar ranar Litinin.

Wasu kafofin yada labarai sun rawaito Abdallah Hamdok, na mai kira ga jama’ar kasar da kada su yarda da juyin mulkin, yayin da ita ma kungiyar kwararru a kasar ta yi kira ga jama'a da su fito kan tituna domin bijirewa juyin mulkin.

Ita ma kungiyar kasashen Larabawa ta nuna damuwa kan abinda ke faruwa a Sudan, inda sakatare Janar na kungiyar Ahmed Aboul Gheit ya yi kira ga bangaroran da ba sa ga maciji a Sudan da su martaba yarjejeniyar da aka kulla da gwamnatin riko.

342/