24 Oktoba 2021 - 20:33
​Tawagar Kwamitin Tsaron MDD Ta Fara Ziyara A Mali

Wata tawagar Kwamitin Sulhu na MDD, ta fara wata ziyarci aiki ta kwana biyu a kasar Mali a kokarin ganin sojojin da suka kwace mulki sun mika ragamar mulki ga hannun gwamnatin farar hula.

Wakilan Kwamitin za su tattauna da sojojin dake rike da mulki a kokarin shawo kan su na mayar da kasar kan tafarkin demokradiyya.

Tawagar wacce kasar Kenya da ke rike da shugabancin kwamitin tsaron MDD na watan Oktoba ke jagoranta za ta gana da da shugaban riko na Mali, Kanal Assimi Goita, da kuma gungun kungiyoyi masu dauke da makamai wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta 2015 da kuma kungiyoyin farar hula.

A nata bangare Mali, ta ce babban makasudin ziyarar shi ne duba halin da kasar ke ciki ta fuskar siyasa, tsaro da kuma ayyukan jin kai.

MDD dai na ganin akwai bukatar daukar matakin daidaita kasar kafin samun galaba kan gungun kungiyoyi masu dauke da makamai.

Kwamitin na fatan ganin sojojin sun bayar da hadin kai, a tsayar da ranar da kasar za ta gudanar da babban zabe.

Tunda farko dai hukumomin Malin, sun yi alkawarin mika mulki cikin watanni 18, saidai a yanzu an bayyana cewa suna tunanin tsawaita mulkin na rikon kwarya.

Ziyarar ta kwanitin tsaron na MDD, na zuwa ne a daidai lokacin da aka fuskantar tada jijiyoyin wuya tsakanin Mali da kuma wasu kasashen turai kan rahotanin cewa sojojin dake rike da mulki a Malin na kokarin kulla kawance da sojojin haya na kasar Rasha na kamfanin Wagner.

342/