Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Mista Putin, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a karshen taron tattaunawa ta club din Valdai da aka gudanar a birnin shakatawa na Sochi.
Putin ya kuma ce "Rasha tana tattaunawa da dukkan bangarorin siyasa a Lebanon kuma za ta ci gaba da yin hakan."
A daye bangaren ya ce Rasha, n afatan samun matsaya guda don cimma yarjejeniya tsakanin bangarorin Lebanon ba tare da zubar da jinni ba."
Kalaman nasa na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan kashe mutum 7 tare da jikkata wasu 60 yayin zanga-zangar lumana a Beirut.
342/