Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Al-Manar ya nakalto Sayyid Safiyuddin shugaban majalisar zartarwa na kungiyar yana jawabi a jana’izar. Sayyid Safiyuddin ya ce kissan ranar Alhamis aiki ne wanda ofishin jakadancin Amurka a birnin Beirut ya shirya. Sannan ‘yan kanzakinta daga wasu ‘yan siyasa a kasar Lebanon suka aiwatar.
Malamin ya kara da cewa kungiyar Hizbullah ta dade ta na yiwa mutanen kasar Lebanon gargadi kan masu neman dawo da yakin basasa kasar. Ya ce abinda ya faru a ranar Alhamis wani makirci ne na son jefa kasar cikin yakin basasa, da kungiyar ta maida martani.
342/