16 Oktoba 2021 - 17:24
Shugaban Kasar Labanon Ya Sha Alwashin Hukumta Wadanda Suka Kashe Masu Zanga-Zangar Lumana

Rahotanni da suka fito daga birnin Berut sun bayyana cewa shugaban kasar Labanon Makel Aun ya yi Alkawarin hukumta duk wanda ke da hannun wajen harin da aka kai wa masu zanga-zangar lumana a birnin Berut.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Auna ya fadi cewa kundin tsarin mulkin kasar shi ne kwai mafita ga matsalolin da kasar ke fuskanta amma ba za’a amince da yin amafani da makami kan masu zanga-zanga ba, domin gwamnati ta bada yanci fadin albarkacin baki

Wannan yana zuwa ne bayan da wasu al’ummar kasar Labanon suna gudanar da zanga- zangar lumana ta nuna rashin amincewa da matakin da Tariq Bitar alkalin da ke bincike kan fashewar gabar tekun Berut yake dauka da ya afku a watan Agustan shekara ta 2020 da ta gabata, inda wasu masu dauke da makamai daga saman bene suka bude wuta kan masu zanga zangar tare da kashe mutane 6 da kuma jikkata fiye da 60,

Kungiyar hizbullah da Amal da ke kasar Labanon sun bukaci magoya bayansu da su kwantar da hankalim kada su dauki doka a hannu kan harin da magoya bayan Jam’iyar AlQuwwat Alibananiya wato Labanes Forcess suka kai kan masu zanga zangar.

342/