13 Oktoba 2021 - 13:46
Wasika Daga Da Wani Malami Da Aka Yankewa Hukuncin Daurin Rai Da Rai A Gidan Yarin Bahrain Zuwa Ga Sheikh Isa Qasim

Wasika Daga Da Wani Malami Da Aka Yankewa Hukuncin Daurin Rai Da Rai A Gidan Yarin Bahrain Zuwa Ga Sheikh Isa Qasim.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti (AS) -ABNA- ya kawo cewa: Sheikh Ali Salman, babban sakataren Qungiyar Al-Wefaq, wanda ke zaman daurin rai-da-rai a cikin kurkukun gwamnatin Al-Khalifa, ya jaddada a cikin wani sako zuwa ga Ayatullah Sheikh Isa Qasim: Ku ci gaba kan abin da Allah ya shiryar da ku. Lalle muna tare daku akan wannan hanya.

Matanin wasikar Sheikh Ali Salman Yazo kamar haka:
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai
Zuwa ga Ayatullah Sheikh Isa Qassem (Allah ya kara kare shi);
Assalamu alaikum wa rahamatul Lahi wa barakatuhu
Allah ya saka muku da alheri
Da fatan Allah ya sake sada mu kusa da ku cikin alheri da da ayyuka nagari.
Ku ci gaba da tafiya akan abin da Allah ya shiryar da ku, lalle muna goyon bayanku akan wannan hanya.
Mun same ka cikin salihin bawa, masanin shari’a, mai tsantsan da kai, mai hikima, mai hankali, mai haƙuri, mai gaskiya da sanin abubuwa game da al’amurran zamanin ka, kamar yadda babu wani shubuha ko shakku a cikin al’amuran zamanin ku da zai afka muku ya rinjaye ku.
Mun same ka kana mai biyayya ga umurnin Allah Madaukakin Sarki, akan wannan hanyar, masu laifin da tayar da hankali ba sa gabanku.
Kamar yadda muka same ka a matsayin jagora mai kishin kasa, mai tausayi, mai kirki da kishin kasa, kun yi kokari kuma ku yi aiki da gaske tukuru da ikhlasi a rayuwar ku don daukakar kasar haihuwa, ci gabanta da kyautatawa dukkan 'ya'yanta.
Kullum kun kasance kuna masu kira zuwa ga gaskiya, adalci, da daidaito ta hanyar gwagwamaya ta lumana da wayewa.
Zuciyarku da hannayenku koyaushe a buɗe suke don yin shawarwari da bin muradun jama'a da burin mutane, burin da ke tasowa daga mutuntaka wanda ya kasance cikin sahihancin siyasa da ke ba wa mutane damar gudanar da nau’oin ayyukansu na doka da zartarwa. Sahihin tsarin tattalin arziki, siyasa, zamantakewa, da tsaro, kwanciyar hankali da ci gaba mai ɗorewa.
Mun same ku amatsayin fitila mai shiryarwa, don haka ku dogara ga Allah, kuma ku zama jagorori da masu shiryarwa ku zamo wadanda zasu karba maku da sauraron ku. Allah yana tare da ku kuma shine mai taimakon ku a cikin abin da zai amfanar da mutane cikin addininsu da duniyarsu, da gyara lamurransu da lamuran al'ummar kasa a halin yanzu da nan gaba, in Allah ya yarda.
Ali Salman
Gidan yarin Joe
19 Mihr 1400/11 Oktoba 2021

342/