Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A loacin da yake zantawa da tashar talabijin CNBC a daren jiya, Ministan harkokin wajen kasar Iran Hussain Amir Abdollahian ya bayyana cewa, Amurka tana da’awar cewa a shirye take ta dawo cikin yarjejeniyar nukiliya da aka cimma kan shirin Iran, amma har yanzu Iran tana da shakku kan kyakkyawar niyyar Amurka dangane da hakan.
Ya ce tun bayan da Amurka ta fice daga cikin yarjejeniyar, har yanzu ba ta koma ba, kuma ko da ta koma kamar yadda sabuwar gwamnatin kasar ta Amurka ta yi alkawalin yin hakan, shin a shirye take ta yi aiki da abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa, ko kuwa za ta yi gaban kanta ne, shi ne abin da Iran ba ta da tabbaci a kansa.
Abdollahian ya ci gaba da cewa, yana zaton Iran za ta koma tattaunawar Vienna nan ba da jimawa ba, amma a halin yanzu tana bin diddigin zaman da aka gudanar ne a lokutan baya daya bayan daya, kafin yanke lokacin komawa zuwa ga tattaunawar.
Iran dai ta jingine yin aiki da wasu bangarorin yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da ita da manyan kasashen duniya ne, bayan da ta zargi wasu bangarorin yarjejeniyar musamman kasashen turai, da kin cika alkawullan da suka rattaba hannu a kansu.
Bayan nan kuma Iran ta dakatar da wasu ayyukan bincike da sanya ido na hukumar IAEA a tashoshin na nukiliya, tare da kara ninka yawan sanadarin uranium da take tacewa zuwa fiye da kashi 60%, wanda kasashen turan ke fargaban cewa Iran din za ta iya kera makaman kare dangi da shi.
342/