Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shafin yanar gizo na labarai Naijanews ya nakalto shugaban hukumar Zaben na kasa Prof. Mahmud Yakub ya na fadar haka a jiya Jumma’a a Abuja, ya kuma kara da cewa tuni an shafe rijista na biyu da suka yi, sannan za’a barsu su yi zabe ne kawai da katinsu na farko. Prof. Yakub ya ce ana aikin gano masu rijista sau biyu a duk fadin kasar.
Labarin ya kara da cewa ya zuwa ranar 5 ga watan Satumban da ya gabata mutane 77,475 ne suka yi rijistan karban sabon katunan zabe, wanda jimillar katunan zaben a Jihar Anambra tun shekara ta 2019 sun kai 2,525,471. A ranar 6 ga watan Nuwamba da muke ciki ne dai za’a gudanar da zaben gwamna a jihar.
342/