Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Mutane da dama ne suke karkashin gine -gine da suka rufta sakamakon girgizar kasar , wata mata da ‘ya’yan ta guda 6 suna daga cikin wadanda abin ya ritsa da su kuma sun rigamu gidan gaskiya.
Ministan cikin gida na kasar ta Pakistan Mir zia ullah Langau ya ce labaran da muke samu sun nuna mutane 20 sun rasu sakamakon girgizar kasar, tuni Ma’aikatan Agaji suke ci gaba da kokarin zakulo mutane da gine –gine suka danne , ko kuma suka makale acikin burabutsai.
342/