5 Oktoba 2021 - 14:26
​Libya: Ana Tsare Da Bakin Haure Da 'Yan Gudun Hijira Kimani 5,000 A Kasar

Wata kungiyar kare hakkin biladama ta kasar Noway ta bada sanarwan cewa jami’an tsaro a kasar Libya suna tsare da ‘yan gudun hijira da bakin haure kimani 5000 a cibiyoyin tsaresu daban daban a cikin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : nakalto wani ma’aikacin kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar Norway mai suna Alexandra Saieh ya na fadar haka.

Ya kuma kara da cewa daga ranar jumma’an da ta gabata jami’an tsaro a kasar Libya sun kama bakin haure da ‘yan gudun hijira kimani 5,000 daga cikinsu akwai mata da yara da dama.

Alexandra Saieh ya kara da cewa wannan wata matashiya ce ga kasashen Turai don su dauki matakin kawo karshen kwararar ‘yan gudun hijira daga kasashen arewacin Afirka zuwa Turai.

Har’ila yau gwamnatin kasar Libya ta tabbatar da cewa ta na tsare da mutane akalla 4,000 a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, kuma ‘yan gudan hijira ne da bakin haure daga kasashe daban daban.

342/