4 Oktoba 2021 - 13:27
​Iran Ta Bukaci Amurka Ta Saki Kadarorinta Da Take Rike Da Su

Ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Abdullahiyan shi ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da gidan talabijn din kasar, inda ya kara da cewa domin nuna kyakkawar niyarta ta koma teburin tattaunawar da aka ake yi kan shirin nukiliyar Iran ya kamata ta saki Akalla dala biliyan 10 da take rike da shi mallakin kasar Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Har ila yau yayi gargadin cewa: “Iran za ta kai karar kasar Koriya ta Kudu idan ta ci gaba da kin bayan bashin da take binta kusan dala miliyan 8 na danyen manfetur din ta da ta saya, tuni aka rufe dukkan asusun ajiyar kasar Iran dake koriya ta kudu

A wata hira ta wayar tarho da yayi da takwaransa na koriya ta kudu chung Eui –Yong , ya bukaci koriya da ta saki kadarorin Iran da aka toshe domin samun damar yin amfani da su cikin gaggawa.

Matsin lambar Amurka kan kasar Koriya ta kudu ne ya jawo daukar wannan matakin amma duk da haka ba za mu ci gaba da zuba ido ba, zamu umarci babban bankin kasar ya dauki matakin da ya dace kan bankuna biyu na kasar Koriya da ake da Asusun ajiya a ciki.

342/