4 Oktoba 2021 - 13:26
​Aljeriya Ta Haramtawa Jiragen Sojin Faransa Ratsawa Ta Sararin samaniyar Kasar

Kasar Aljeriya, ta sanar da haramta wa jiragen sojin Faransa keta sararin samaniyarta, a wani lamari dake nuna yadda dangantaka tsakanin kasashen biyu ke kara tsami.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Dama dai Aljeriya ta janye jakadanta a Faransa domin shawartawa, bayan wani furici da aka nakalto shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi, game da tarihin samun ‘yancin kan Aljeriya, wanda kuma bai yi wa mahukuntan Aljeriyar dadi ba.

Dama dai an fuskanci tada jijiyoyin wuya tsakanin mahukutan Paris da na Algers bayan da Faransa ta tsaurara matakan bada takardar visa ga ‘yan kasashen Larabawan yankin Magreb daga ciki har da ita Aljeriyar.

Faransa dai na amfani da sararin samaniyar Aljeriya, wajen isa ko fita yankin Sahel inda ta ke da dakaru na rundunar Barkhane, sai dai ta ce hakan ba zai kawo mata wata matsala ba wajen tafiyar da aikinta a yankin ba.

342/