29 Satumba 2021 - 15:37
​Iraki: Mutane Miliyon 16 Ne Suka Halarci Juyayin 40 Na Imam Husain (a)

Hukomomi masu kula da wurare masu tsarki a kasar Iraki sun bayyana cewa mutane kimani miliyon 16 ne suka sami damar halattar juyayin 40 na shahadar Imam Husain (a) a birnin Karbala.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran ya nakalto hukumomi masu kula da wurare masu tsarkin na cewa sun fito daga kasashen duniya daban-daban, sannan daga kasar Iran kadai mutane kimani dubu 90 suka sami halattar juyayin, bayan da hukukomin kasar Iraki suka takaita adadin zuwa dubu 60 kacal da farko.

Juyayin arba’in na wannan shekara dai, wato ranar 20 ga watan Safar na shekara ta 1443 H.K ta zo dai dai da 27 ga watan Satumban shekara ta 20121M. ranar da sarakunan bani umayya suka kashe Imam Husain (a) limami na 3 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Allah (s). da iyalan gidansa da kuma sahabbansa a karbaka a ranar 10 ga watan Muharam na shekara ta 61 bayan hijira.

Wannan taron shi ne taro mafi girma irinsa na duniya a halin yanzu. A wani labarin kuma jami’an tsaro na Hashdushaabi na kasar ta Iraki sun bayyana cewa an kammala juyayin arbi’an a kasar ba tare da fuskantar matsalolin tsaro ba .

342/