27 Satumba 2021 - 11:15
Iraki: An Fara Tarukan Arbaeen Na Imam Hussain (AS)

A yau ne ake gudanar da tarukan ziyarar arbaeen na Imam Hussain (AS) a birnin Karbala na kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran Mawazin News na kasar Iraki ya bayar da rahoton cewa, tun a cikin kwanakin da suka gabata ne miliyoyin masu ziyara suka fara isowa birnin na Karbala domin halartar wadannan taruka.

A yau ne rana ta 20 ga watan Safar ake gudanar da irin wadannan taruka a kowace shekara, tare da halar miliyoyin masoya ahlul bait daga ciki da wajen kasar ta Iraki.

A shekarar bana ma kamar shekarar da ta gabata, an dauki kwararan matakai kan batutuwa na kiwon lafiya, ganin cewa har yanzu akwai sauran barazanar cutar corona, wadda za ta ita yaduwa a tsakanin masu ziyara.

Baya ga haka kuma a bangaren tsaro ma an dauki kwararan matakai na tsaro, inda dubban jami’an tsaron kasar a cikin shirin ko ta kwana suke sintiria ko’ina, tare da kafa shingayen bincike.

A kowace a irin wannan rana ana gudanar da tattaki daga birane daban-daban na kasar zuwa birnin na Karbala domin halartar tarukan arbaeen na Imam Hussain (AS) taron da ya kwashe fiye da shekaru dubu daya da dari uku ana gudanar da shi.

342/